Zaben Najeriya: Wasu 'yan tsagera sun kona kayayyakin zabe a Bayelsa
Wasu ‘yan tsagera sun karbe, tare da kona kayayyakin zabe na wasu mazabu 3 a jihar Bayelsa dake kudu maso kudancin Najeriya a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jihohi da ke gudana a kasar a halin yanzu.
Wallafawa ranar:
Yanzu haka jami’an hukumar zaben kasar da aka tura aiki a yankin Ogbia sun koma Yenagoa, babban birnin jihar don su tsira da lafiyarsu ganin yadda ‘yan jagaliya suka rikita yankin.
Rahotanni na nuni da cewa jam’iyyun PDP da na APC na takarar kujerar majalisar dokokin yankin, kuma dukkanin jam’iyyun na neman rinjye a majalisar dokokin jihar, gabanin zaben gwamnan jihar da za a yi a 11 ga watan Nuwamba.
Jami’in wayar da kan al’umma na hukumar zaben jihar Bayelsa din, Mr Wilfred Ifogah, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin.
A lokacin wallafa wannan rahoto, alamu na nuni da cewa zabe ba zai yiwu a mazabar Ogbia ta 2 ba, duba da cewa jami’an INEC sun riga sun koma Yenagoa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu