Isa ga babban shafi
KAI-TSAYE: SAKAMAKON ZABEN GWAMNONIN NAJERIYA

Sakamakon zaben gwamnonin jihohin Najeriya

Wannan shafin zai rika kawo muku kammalallen sakamakon zaben gwamnoni da aka gudanar a jihohin Najeriya da Hukumar Zaben Kasar ta fitar da kanta.

Babban Dakin Tattara Sakamakon Zaben Najeriya da ke birnin Abuja.
Babban Dakin Tattara Sakamakon Zaben Najeriya da ke birnin Abuja. AP - Ben Curtis
Talla

JIHAR BAUCHI

Gwamnan Bauchi Sanata Bala Muhammad ya samu nasarar yin tazarce a zaben da ya gudana a ranar Asabar 18 ga watan Maris. Hukumar zabe ta ce Sanata Bala Muhammad ya samu kuri'u dubu  525,280, yayin da abokin hamayyarsa na APC tsohon shugaban hasfan sojin saman Najeriya mai ritaya Air Marshal Sadik Baba Abubakar ya samu kuri'u 432,272.

 


JIHAR NASARAWA

Gwamna mai ci Abdullahi Sule yayi tazarce, bayan sake lashe zaben kujerar gwamnan da yayi da kuri’u dubu 347,209, inda ya doke abokin hamayyarsa David Ombugadu na jam’iyyar adawa ta PDP da ya samu kuri’u dubu 283 da 016


JIHAR KANO

Hukumar zaben Najeriya ta bayyana dan takarar jam'iyyar NNPP Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano da kuri'u miliyan 1 da dubu 19 da 602, yayin da dan takarar jam'iyyar APC Nasir Yusuf Gawuna ya samu kuri'u dubu 890,705.


JIHAR YOBE

Gwamna Mai Mala Buni na APC ya ci gaba da rike madafun iko bayan ya yi nasara a zaben gwamna na ranar Asabar da yawan kuri'u 317,113 , inda ya yi wa babban mai fafatawa da shi na jam'iyyar PDP, Alhaji Sharif Abdallah fintinkau wanda kuma ya samu jumullar kuri'u 104,259. 


JIHAR KWARA

Sakamakon Hukumar INEC ya nuna cewa, gwamna mai ci na jihar Kwara,  AbdulRahman AbdulRazaq na jam'iyyar APC, shi ne ya lashe zaben ranar Asabar da yawan kuri'u 273,424, inda ya doke babban abokin hamayyarsa na PDP, Alhaji Abdullahi Shu'aib Yaman wanda ya samu kuri'u 155,49490.


JIHAR GOMBE

Gwamna mai ci, Inuwa Yahya na jam'iyyar APC shi ne ya sake lashe zaben jihar Gombe daa yawan kuri'u 342, 821, inda Muhammad Baarde na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 233, 131.


JIHAR OGUN

Hukumar zaben Najeriya ta ayyana Dapo Abiodun na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ogun da yawan kuri'u 276,298, inda ya doke abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Ladi Adebutu wanda ya samu kuri'u 262,383.


JIHAR LAGOS

Gwamnan Lagos Baba Jide Sanwo-Olu na jam'iyyar APC ya samu nasarar zarcewa bisa shugabancinsa, bayan da hukumar zabe ta bayyana cewar ya lashe kuri'u dubu 762,134, inda ya doke manyan abokan hamayyarsa Olajide 'Jandor' Adediran na PDP wanda ya samu kuri'u 62,449 da Gbadebo Rhodes-Vivour na jam'iyyar LP mai kuri'u  dubu 312,329.


JIHAR KATSINA

Hukumar zaben Najeriya INEC ta ayyana Dakta Dikko Umaru Radda na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Katsina.

Radda ya samu nasara ne da ƙuri'u 859,892, yayin da mai biye masa Garba Yakubu Lado Danmarke na jam'iyyar PDP ya samu kuri'a 486,620.

Jami'in da ke tattara sakamakon zaɓen gwamnan a jihar ta Katsina, Farfesa Mu'azu Abubakar Gusau ne ya bayyana sakamakon a daren wannan Lahadi.


JIHAR JIGAWA

Mataimakin gwamnan jihar Jigawa kuma ɗan takarar gwamnan a karkashin jam'iyyar APC mai mulki, Alhaji Umar Namadi ya lashe zaɓen gwamna da aka gudanar a ranar Asabar.

Namadi ya lashe zabe a ƙananan hukumomi 26 daga cikin 27 na jihar.

Ya samu nasarar ce da kuri'u 618,449 yayin da dan takarar jam'iyyar PDP, Mustapha Sule Lamido ya zo na biyu da kuri'u 368,726 sai kuma Aminu Ibrahim na NNPP ya zo na uku da ƙuri'u 37,156.


JIHAR OYO

Tun kafin farko Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya, INEC ta ayyana Seyi Makinde na Jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a jihar Oyo a zaɓen ranar Asabar da aka gudanar.

Makinde wanda shi ne gwamna mai ci a jihar ta Oyo ya samu ƙuri'u mafi yawa inda ya bai wa babban ɗan adawa a jihar, Teslim Folarin na Jam'iyyar APC tazarar ƙuri'u dubu 300.

INEC ta ce Seyi Makinde ya samu ƙuri’u 563,756 yayin da Teslim Folarin na APC ya samu ƙuri'u 256,685.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.