Isa ga babban shafi
Zaben Najeriya na 2023

Kuri'un Fufore zasu fayyace nasara ko akasi ga Binani na APC

Gwamnan jihar Adamawa kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Ahmadu Fintiri, ya ci gaba da kasancewa kan gaba a zaben gwamna a halin yanzu bayan bayyana sakamakon zaben kananan hukumomi 20 daga cikin 21 dake jihar.

Sanata Aishatu Binani 'Yar takarar neman gwamnan jihar Adamawa a Nijeriya
Sanata Aishatu Binani 'Yar takarar neman gwamnan jihar Adamawa a Nijeriya © Bashir Ahmad
Talla

To sai dai Aishatu ‘Binani’ Dahiru, ‘yar takarar jam’iyyar APC, na ci gaba da fatan zama mace ta farko da aka zaba a matsayin gwamnan jihar dama  Najeriya baki daya. Kuma wannan fata nata ya ta'allaka ne da sakamakon zaben Fufore, karamar hukuma daya tilo da ba a bayyana sakamakonta ba a hukumance.

Daga sakamakon da aka bayyana kawo yanzu, Mista Fintiri ne ke kan gaba da kuri'u sama da 35,000.  Yayin da yake da kuri'u 401,113, Binani na biye masa da kuri'u 365,498.a

Jam’iyyar APC za ta bukaci ta zarce tazarar kuri’u da ake da ita a yanzu domin a bayyana ta a matsayin wadda ta lashe zaben jihar.

Mista Fintiri ya yi nasara a kananan hukumomi 13 yayin da Binani ta samu nasara a bakwai daga cikin 20 da aka ayyana ya zuwa yanzuu

Tuni jam'iyyun na PDP da APC suka fara nuna wa juna yatsa tare da zargin juna da yunkurin sauya sakamakon zaben karamar hukumar Fufore.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.