Isa ga babban shafi

NNPP ta lashe zaben gwamnan Kano, na Kebbi bai kammala ba

Hukumar zaben Najeriya ta yi nisa wajen bayyana sakamakon zaben gwamnoni da na ‘yan majalisunsu da aka yi a jihohin kasar 28 daga cikin 36.

Magoya bayan jam'iyyar NNPP a jihar Kano.
Magoya bayan jam'iyyar NNPP a jihar Kano. AP - Sani Maikatanga
Talla

Sakamako na baya bayan nan da aka sanar dai shi ne na Kano, inda jam’iyyar adawa ta NNPP ta lashe zaben kujerar gwamnan jihar.

Da fari dai an shiga zaman dar-dar a Kanon, musamman bayan dokar hana fitar da gwamnati ta kafa da safiyar wannan Litinin yayin da ake dakon sakamakon karshe kan wanda yayi nasara.

Bayan jinkirin da aka samu ne kuma duk da kammala sanar da sakamakon da aka tattara daga dukkanin kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar, daga karshe hukumar zabe ta bayyana dan takarar jam'iyyar NNPP Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben na Kano da kuri'un da yawansu ya kai miliyan 1 da dubu 19 da 602, yayin da dan takarar jam'iyyar APC Nasir Yusuf Gawuna ya samu kuri'u dubu 890,705.

Daga cikin sauran jihohin da zabensu ya kammala har aka sanar da ‘yan takarar da suka yi nasara akwai Yobe inda Gwamna Mai Mala Buni na jam'iyyar APC ya cigaba da rike madafun iko bayan lashe kuri'u dubu 317,113. A Gombe ma gwamnan mai ci, Inuwa Yahya na jam'iyyar APC ne ya sake lashe zaben jihar da kuri'u 342, 821.

Sai jihar Ogun, inda Dapo Abiodun na APC ya lashe kujerar gwamna da kuri'u 276,298.

A Oyo gwamna mai ci Seyi Makinde ne na PDP ya lashe zaben da aka yi da kuri’u 563,756 yayin da Teslim Folarin na APC ya zo na biyu da kuri'u 256,685.

Kawo yanzu dai hukumar zaben Najeriya ta sanar kammalallen sakamako tare da ‘yan takarar da suka yi nasara a jihohi 11, yayin da ake dakon yadda za ta kaya a ragowar 17.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.