Isa ga babban shafi

Jam’iyyar PDP ta yi wa APC bazata a jihar Zamfara

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle na jam’iyyar APC, ya rasa kujerarsa ga dan takarar jam’iyyar PDP Dauda Lawal a zaben kujerar gwamnan jihar da ya gudana a ranar Asabar 18 ga watan Maris.

Gwaman jihar Zamfara Bello Matawalle
Gwaman jihar Zamfara Bello Matawalle © Zamfara State
Talla

Hukumar zabe mai zaman kanta ta ce Dauda Lawal ya  samu nasarar zama zababben gwamna mai jiran gado ne bayan lashe kuri’un da  yawansu ya kai 377,726, yayin da  gwamna Matawalle ya samu 311,976.

Kafin sanar da sakamakon zaben jihar ta Zamfara dai, an fuskanci tsaikon isowar sakamakon kuri’un da aka kada a karamar hukumar Maradun, inda aka fara yada jita-jitar cewa ‘yan bindiga ne suka sace Dakta Ahmed Kainuwa babban jami’in zaben da ke tafe da sakamakon yankin da aka tattara.

Sakamakon na Zamfara dai na daga cikin wadanda suka fi bayar da mamaki a zabukan kujerar gwamnan da aka yi a karshen makon da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.