Isa ga babban shafi

INEC ta sanar da ranar sake zabe a Kebbi da Adamawa

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Najeriya INEC ta bayyana ranar da za a sake gudanar da zabukan jihohin Kebbi da Adamawa. 

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu REUTERS - REUTERS TV
Talla

Babban Sakataren Yada Labarai na INEC, Mista Rotimi Lawrence Oyekanmi ne, ya bayyana hakan a birnin Abuja. 

Ya ce za a gudanar da zabukan gwamnoni da na wasu ‘yan majalisar tarayya da na jihohi a rana guda. 

Yayin taron da ta gudanar a ranar Litinin, INEC ta yanke shawarar cewa za a gudanar da dukkanin zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun tarayya da na jihohi a ranar Asabar, 15 ga Afrilu, 2023,” in ji Oyekanmi. 

 

Ya ce nan ba da jimawa ba za a fitar da cikakken bayani kan yadda zaben zai gudana a hukumance. 

Rahotanni sun nuna cewa zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu da kuma zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi na ranar 18 ga watan Maris, an soke zabukan wasu mazabun, abin da ya sanya INEC ayyana sakamakon wasu jihohin a matsayin wadanda ba su kammala ba. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.