Isa ga babban shafi

Peter Obi ya ci amanar Najeriya - Inji gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta zargi dan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar Labor, Peter Obi da cin amanar kasa tare da kuma tunzura jama’a domin jefa kasar cikin rikici bayan ya fadi a zaben 2023.

Peter Obi
Peter Obi © Daily Post
Talla

Ministan Yada Labarai da Al’adu na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed da ke zanta wa da wasu manya kafafen yada labarai na duniya a birnin Washington DC na Amurka, ya  bayyana haka.

Ministan ya ce, babu yadda Obi da mataimakinsa Datti Ahmed za su ci gaba da yi wa ‘yan Najeriya barazana kan cewa, muddin aka rantsar da zababben shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a ranar 29 ga watan Mayu, to hakan na nufin kawo karshen demokuradiya.

Wannan cin a amanar kasa ne. Ba za ku ci gaba da gayyato ta’addanci ba. Kuma abin da suke aikatawa kenan. Inji Lai.

Wannan na zuwa ne bayan fallasar wani faifen murya wanda a cikinsa aka jiyo muryar da aka ce ta Mista Obi ce na bayyana zaben 2023 a matsayi yaki na addini, al'amarin da ya yamutsa hazon siyasar Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.