Isa ga babban shafi

Aminu Jaji ne ya fi cancantar zama shugaban majalisa - 'Yan arewa mazauna kudu

'Yan arewa mazauna jihohi 17 na kudancin Najeriya sun bayyana Hon. Aminu Sani Jaji na jihar Zamfara a matsayin wanda ya fi cancantar zama shugaban Majalisar Wakilan kasar ta 10 a daidai lokacin da ake rade-radin cewa, akwai yiwuwar Hon. Ahmed Idris Wase na jihar Filato ya maye wannan mukamin. 

Hon. Aminu Sani Jaji, dan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Zamfara
Hon. Aminu Sani Jaji, dan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Zamfara © Daily Post
Talla

A wani taron manema labarai da suka gudanar a birnin Lagos a ranar Talata, 'yan arewacin kasar mazauna kudanci karkashin jagorancin Alh. Sa'adu Yusuf Dandare Gulma, shugaban jam'iyyar APC na 'yan arewa a Lagos, sun ce, Aminu Jaji na da kwarewa duk kuwa da karancin shekarunsa.

Ku latsa bidiyon da ke kasa domin kallon taron manema labaran na 'yan arewa a Lagos

Aminu Jaji ne ya fi cancantar zama shugaban majalisar Najeriya - Inji 'yan arewa a kudu
Taron manema labarai na 'yan arewacin Najeriya mazauna kudancin kasar a Lagos.
Taron manema labarai na 'yan arewacin Najeriya mazauna kudancin kasar a Lagos. © RFI/ Abdurrahman Gambo

Koda yake wasu na ganin cewa, Hon. Wase na kan gaba dangane da samun wannan mukami na kakakin majalisar wakilan.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen rantsar da Majalisar Wakilan Najeriya ta 10 bayan gudanar da zabukan 2023.

Ana iya cewa, lokaci ne kadai zai fayyace ainihin wanda zai maye gurbin Femi Gbajabiamila na jihar Lagos wanda ya dare kujerar shugabancin majalisar wakilan tun a shekarar 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.