Isa ga babban shafi

Najeriya: An kashe mutane 46 a wani sabon hari da aka kai jihar Benue

Akalla mutane 46 da suka hada da dan shugaban karamar hukumar Otukpo da dan sanda daya aka kashe a yammacin Laraba, a wani hari da wasu da ake kyautata zaton makiyaya ne dauke da makamai suka kaddamar a kauyen Umogidi da ke gundumar Enetekpa Adoka a karamar hukumar Otukpo ta jihar Benue.

Alamar 'Yan bindiga masu kashe mutane babu kakkautawa a Najeriya
Alamar 'Yan bindiga masu kashe mutane babu kakkautawa a Najeriya © Daily Trust
Talla

Rahotanni sun ce, adadin wadanda suka mutu na iya zarta haka saboda mutane da dama sun tsere, kuma har yanzu ana ci gaba da laluben inda suka makale.

Harin dai ya zo ne bayan wani hari da aka kai wa wannan al’umma a baya wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku kuma lokacin da makiyayan dauke da muggan makamai suka afka wa al’ummar a karo na biyu cikin kasa da sa’o’i 12, ba a jima da binne gawawwakin wadanda suka kashe ba

Shugaban karamar hukumar Otupko, Mista Bako Eje wanda dan kauyen ne kuma aka kashe dansa a harin ya koka da yadda maharan ke kokarin mamaye musu yankuna.

A cewar Mista Eje, bayan harin da aka kai a baya wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku, sun je ziyara kauyen ne domin halartar jana’izar gawawwakin, lokacin da maharan suka aukawa dansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.