Isa ga babban shafi

Babu mahalukin da zai hana rantsar da Tinubu - Umahi

Gwamnan Jihar Ebonyi da ke Najeriya, David Umahi ya ce babu wani mahaluki a bayan kasa da zai hana rantsar da zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa. 

A ranar 29 ga watan Mayun wannan shekara za a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban Najeriya.
A ranar 29 ga watan Mayun wannan shekara za a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban Najeriya. REUTERS - JAMES OATWAY
Talla

Yayin da yake tsokaci kan masu rade-radin cewar bai dace a rantsar da sabon shugaban ba da kuma masu neman ganin an kafa gwamnatin rikon kwarya, Umahi ya ce tun kafin gudanar da zabe ya shaida wa duniya cewar babu abin da zai hana Tinubu samun nasara, saboda haka a halin yanzu bai ga dalilin kuma da zai sa a dakatar da rantsar da shi ba. 

Gwamnan ya ce ganin irin shingayen da ya yi ta tsallakewa har zuwa wannan lokacin da ya samu nasara, babu wani dalilin da zai hana rantsar da Tinubu a watan gobe. 

Yanzu haka jam’iyyun PDP da Labour na kotu inda suke kalubalantar nasarar da Tinubu ya samu a zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 25 ga watan Fabarairun da ya gabata. 

Hukumomin tsaron Najeriya sun ja kunnen masu tsokaci kan kafa gwamnatin rikon kwarya da su shiga taitayinsu, yayin da tuni aka fara shirin mika mulki wajen kafa kwamitoci kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. 

Umahi da ke kammala wa’adin mulkinsa na shekaru 8 a matsayin gwamnan jihar Ebonyi na daya daga cikin masu neman shugabancin Majalisar Dattawa sakamakon nasarar da ya samu na lashe kujerar mazabarsa a zaben da ya gabata. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.