Isa ga babban shafi

Gwamnatin Najeriya ta ce Peter Obi zai sha tambayoyi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa, dan takarar  shugabancin kasar na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, na da wasu dimbin tambayoyi da zai amsu su dangane da wata murya da ta fallasa wadda aka ce ta kunshi hirarsa da shugaban Majami’ar Living Faith, Bishop David Oyedepo.

Peter Obi
Peter Obi © Daily Post
Talla

Bayan ya kwashe tsawon wasu kwanaki bai ce uffam ba dangane da muryar, daga bisani Obi ya fito ya bayyana cewa, murya ta jabu ce, sannan ya zargi gwamnatin tarayya da yi masa sharri.

Sai dai a yayin wani taron manema labarai a birnin London, Ministan Yada Labarai da Al’adu na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed ya kalubalanci Obi da ya yi karin bayani kan kalamansa na cewa, muryar ta jabu ce.

Ministan ya  ce, wannan muryar ta girgiza ‘yan Najeriya saboda yadda aka jiyo Mista Obi na rokon malamin addinin da ya taimaka masa wajen shawo kan Kiristoci har su fahimci cewa, zaben 2023 yaki ne na addini, a don haka su goya masa baya.

Yanzu haka gwamnatin Najeriya ta ce, akwai bukatar Mista Obi ya fito ya yi wa jama’a karin haske kan abin da yake nufi da jabu.

Ana zargin Obi da gina yakin neman zabensa bisa doron addini da kabilanci a Najeriya, yayin da tuni ya sha kashi  a zaben wanda aka ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.