Isa ga babban shafi

APC ta maka Abba Gida-Gida a kotu bayan ya lashe zaben Kano

Jam’iyyar APC reshen jihar Kano da ke Najeriya ta shigar da kara a gaban kotun sauraren korafe-korafen zaben gwamna, inda take kalubalantar Hukumar Zaben Kasar ta INEC kan yadda ta ayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris.

Dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar APC, Nasir Yusuf Gawuna
Dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar APC, Nasir Yusuf Gawuna © Triumph News
Talla

Jam’iyyar ta APC ta ce, Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida bai cancanci tsayawa takara a zaben ba saboda a cewarta, sunansa ba ya cikin jerin sunayen mambobin jam’iyyar NNPP ta aika wa INEC.

Kazalika APC ta yi zargin cewa, NNPP ba ta lashe zaben ba musamman ganin yadda aka kidaya wa jam’iyyar hatta kuri’un da suka lalace a cewarta, kuma tana ganin cewa, da an cire lalatattun kuri'un, da ita za ta yi nasara.

Koda yake, dan takarar gwamnan na jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna bai yi tarayya da jam’iyyar ba wajen shigar da wannan koken.

Tuni dai Gawuna ya amince da shan kayi a zaben wanda sakamakonsa ya nuna cewa, Abba Gida-Gida ya samu kuri’u miliyan 1 da dubu 19  da 602, yayin da shi kuma ya samu kuri’u dubu 890 da 705.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.