Isa ga babban shafi

Najeriya:'Yan sintiri sun kashe 'yan ta'adda 50 a Neja

Rahotanni daga Jihar Neja a tarayyar Najeriya na cewa mutane akalla 50 ne suka rasa rayukan su a karamar hukumar Ibbi, sakamakon wata arangama tsakanin ‘yan sintiri da kuma ‘yan ta’adda da suka addabi wannan yanki. 

'Yan sa kai na taimaka wa jami'an tsaro a yaaki da ta'addanci a Nigeria,.
'Yan sa kai na taimaka wa jami'an tsaro a yaaki da ta'addanci a Nigeria,. © AFP/David McNew
Talla

Ana dai zargin wadannan ‘yan ta’adda sune suka kutsa kai kauyen, a makon jiya, inda suka hallaka mutane da dama, yayin da suka yi garkuwa da guda 12. 

Bincike ya nua cewa ‘yan sintirin ne suka farwa ‘yan ta’addar a maboyar su, yayin da suka hallaka da dama daga cikin su, bayan sun lalata sansanonin su dake kewayen Wajen shakatawa na Kainji, yayin da suka shafe tsahon kwanaki 4 suna artabu da juna. 

Yayin rikicin dai 9 cikin mutane 12n da ‘yan bindigar suka sace a makon jiya sun kubuta cikin su har da magatakardar babbar kotun shari’ar musulunci ta jihar da kuma mata guda 6. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.