Isa ga babban shafi

An gaza sasantawa tsakanin gwamnati da ma'aikatan sufurin jiragen sama

Kungiyoyin kwadago na ma’aikatan fannin sufurin jiragen sama a Najeriya sun sha alwashin rufe ilahirin filayen jiragen saman kasar bayan cikar kwanaki 7.

Fasinjoji a filin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke birnin Lagos.
Fasinjoji a filin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke birnin Lagos. REUTERS - TEMILADE ADELAJA
Talla

Ma’aikatan da suka kauracewa aiki tsawon kwanaki 2 daga ranar Litinin zuwa Talata saboda neman a biyasu hakkokin wasu kudade da suke bin gwamnati, da kuma inganta musu yanayin da suke aiki, da dai  sauran wasu bukatu, sun sha alwashin ne yayin zanga-zangar da suka yi a wani bangare na filin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke birnin Lagos.

Rahotanni sun ce sai da jami’an tsaro suka watsa taron ‘yan kwadagon a lokacin da suka hadu domin gudanar da zanga-zanga a ranar Litinin da ta gabata, bayan da suka fara yajin aikin kwanaki biyu, domin bayyana wa gwamnati bacin rai kan kin amsa bukatunsu.

Tun ranar Litinin ma’aikatar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya ta bukaci ma’aikatan da ke zanga-zanga da su rungumi zabin shiga tattaunawa da gwamnati a yajin aikin da suka shiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.