Isa ga babban shafi

Najeriya: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 16 a Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara dake Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane 16 a wasu hare-haren da suka kai sassan jihar.  

Alamar 'Yan bindiga masu kashe mutane babu kakkautawa a Najeriya
Alamar 'Yan bindiga masu kashe mutane babu kakkautawa a Najeriya © Daily Trust
Talla

Maharan sun kai farmaki ne kan kauyukan Birnin Magaji da Mazauda da Nasarawa da Mai Layi da kuma Gidan Kane, inda suka jikkata mutane da dama bayan wadanda suka halaka. 

Wasu mazauna yankunan suka ce  ‘yan bindigar sun haramta noma a lokacin damina da ke gab da sauka, har sai gwamnati ta janye sojojin da ta girke a wannan yanki. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.