Diphtheria ta kashe mutane 73 cikin 557 da suka harbu da cutar a Najeriya
Hukumar Lafiya ta Duniya, ta ce a Najeriya, akalla mutane sama da dari 5 da 57 ne aka tabbatar sun harbu da cutar diphtheria, wato makarau a jihohi 21 na kasar tun da aka shiga wannan shekarar ta 2023. Haka zalika, adadin wadanda cutar ta kashe ya kai 73. .
Wallafawa ranar:
Kunna - 00:59
Talla
A watan Disambar shekarar 2022, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya da sanar da barkewar cutar diphtheria a jihohin Kano da Legas.
Dr Salihu Ibrahim Kwaifa, kwararren likita a Abujan Najeriya ya yi mana karin bayani a kan wannan cuta, kuma kuna iya latsa alamar sauti domin saurara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu