Isa ga babban shafi

An kafa dokar hana tsadar aure a jihar Sokoto

Majalisar Jihar Sokoto da ke Najeriya ta sanya hannu kan wani kudirin dokar da ke sanya ido kan tsada da almubazzarancin da jama'a ke yi a bikin aure a jihar.

Ango da amarya da kawayenta a Najeriya.
Ango da amarya da kawayenta a Najeriya. Pinterest Social media service
Talla

Kudirin wanda Alhaji Abubakar Shehu na jam'iyyar APC da Faruk Balle na Jam'iyyar PDP suka gabatar, sai da aka fara gabatar da shi ga Kwamitin Kula da Al'amurran Addini a majalisar.

Shehu wanda shi ne shugaban kwamitin, ya gabatar da rahotonsu a wani zaman farko na 'yan majalisar kuma daukacinsu suka amince ya zama doka. 

Kudirin dokar na bukatar sanya ido kan almubazzarancin kudi da ake yi a yayin bikin aure da taron suna da kaciya da sauran bukukuwa a sassan jihar.

Bayan wata muhawara a zaman na farko da mataimakin shugaban majalisar ya jagoranta, Alhaji Abubakar Magaji, kudirin dokar ya samu amincewar 'yan majalisar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.