Isa ga babban shafi

Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da Adeleke a matsayin Gwamnan Osun

Kotun kolin Najeriya, ta tabbatar da Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.

Sabon gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke yayin karbar ragamar jagorancin jihar 27/11/22.
Sabon gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke yayin karbar ragamar jagorancin jihar 27/11/22. © Ademola Adeleke
Talla

Da take zaman sauraron karar da dan takarar gwamnan jihar Osun din Gboyega Oyetola, ya daukaka zuwa gabanta, kotun mai alkalai biyar ta ce karar da aka shigar gabanta bata da kwararan hujjoji.

Kotun karkashin jagorancin mai shari’a, John Inyang Okoro, ta ce Oyetola tare da jam’iyyar APC, sun gaza gabatar da hujjojin da ke cewa na’urar BVAS ta gaza tantance masu kada kuri’a a rumfunan zabe 744, abin da ya haifar da aringizon kuri’u

A watan Yuli ne hukumar zaben Najeriyar INEC, ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe gwamnan jihar ta Osun.

Acewar INEC, Adeleke wanda ya tsaya takarar gwamnan jihar karkashin inuwar jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 403,371, wanda hakan ya bashi nasara akan Adegboyega Oyetola na jam’iyyar PAC da ya samu kuri’u 375,027.

Amma Oyetola, wanda ke neman sake tsayawa takara, ya kalubalanci nasarar abokin hamayyarsa, yayin da ya yi nasara a kotun sauraron kararrakin zabe, sai dai ya sha kaye a kotun daukaka kara da kuma kotun koli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.