Isa ga babban shafi

Tinubu ya gana da kwankwaso a birnin Paris

Zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya gana da Sanata Rabi’u Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a kasar Faransa.

Zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu daga hagu, da kuma Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
Zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu daga hagu, da kuma Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso. © premiumtimes
Talla

Shugabannin biyu sun gana a birnin Paris, inda rahotanni ke cewa sun tattauna batutuwan da suka shafi zaben shugabannin majalisar gabanin kaddamar da babban taron kasa karo na 10 a ranar 13 ga watan Yuni.

Rahotanni sun ce Tinubu ya bar Najeriya ne a ranar Laraba 10 ga watan Mayu zuwa Turai.

Zababben shugaban kasar ya shaida wa Kwankwaso cewa ya tuntubi abokan siyasarsa kan bukatar yin aiki tare.

An ce shugaban mai jiran gado da bakon nasa sun amince da gudanar da taruka game da ci gaban kasar.

Yayin da uwargidan Kwankwaso da Abdulmimin Jibrin, zababben dan majalisar wakilai na jam’iyyar NNPP, suka raka shi wurin taron, uwargidan Tinubu da Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai mai barin gado, na wadanda suka halarci taron.

Zababben shugaban kasar da Sanata Kwankwaso sun yi ganawar sama da sa’o’i 4 a birnin Paris ranar Litinin.

Majiyar ta ce Tinubu ya kuma yi tsokaci kan sasanta Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano da Sanata Kwankwaso.

A shekarar 2015 ne Ganduje ya gaji Kwankwaso, amma ba da dadewa ba suka samu sabani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.