Isa ga babban shafi

Ba zan bai wa 'yan Najeriya kunya ba - Tinubu

Zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya lashi takobin cewa, ba zai bai wa 'yan kasar kunya ba, kalaman da ya furta jim kadan da karramawar da shugaba mai barin gado, Muhammadu Buhari ya yi masa da lambar yabo ta GCFR a fadarsa da ke birnin Abuja a wannan Alhamis.

Bola Ahmed Tinubu tare da Muhammadu Buhari a wurin bikin karrama zababben shugaban kasar a Abuja.
Bola Ahmed Tinubu tare da Muhammadu Buhari a wurin bikin karrama zababben shugaban kasar a Abuja. © Nigeria Presidency
Talla

Tinubu ya ce, ya fahimci ma'anar da wannan lambar yabon ke kunshe da ita da kuma aikin da ke gabansa, yana mai alkawarin cewa, ba zai bai wa Buhari da sauran 'yan Najeriya kunya ba.

Ni mutun ne mai saukin kai wanda ya ci gajiyar goyon-baya da fatan alheri daga mutanen Najeriya. Mutane sun ba ni amana. Ka yi naka ya mai girma shugaban kasa. Inji Tinubu.

Zababben shugaban ya bayyana kudirinsa na mayar da hankali kan bangarorin da suka shafi tsaro da tattalin arziki da noma da samar da ayyukan yi da ilimi da lafiya da wutar lantarki da dai sauransu.

Lokacin da shugaba Buhari ke rataya wa Tinubu lambar yabon.
Lokacin da shugaba Buhari ke rataya wa Tinubu lambar yabon. © Niger presidency

Tinubu ya  bayyana cewa, ba zai aikata kasa da abin da mutane ke tsammani daga wurinsa ba.

Nan da ranar 29 ga wannan wata na Mayu ne ake sa ran rantsar da Tinubu a matsayin sabon shugaban Najeriya bayan ya lashe zaben watan Fabairun da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.