Isa ga babban shafi

APC ta tsayar da malamin Firamare a matsayin dan takarar mataimakin gwamna

‘Dan Takaran Gwamnan Jihar Kogi dake Najeriya a karkashin Jam’iyyar APC, Usman Ododo ya dauki malamin makarantar firamare a matsayin wanda zai zama masa mataimaki a zaben da za’ayi a watan Nuwamba mai zuwa. 

Alamar jam'iyyar APC mai Mulkin Najeriya
Alamar jam'iyyar APC mai Mulkin Najeriya © Bashir Ahmad
Talla

Ododo ya gabatar da Salifu Joel wanda shugaban kungiyar malaman makarantu ta NUT ne a Jihar Kogi, kana kuma ma’aji a kungiyar kwadago ta jihar a matsayin abokin takararsa a zaben mai zuwa. 

Gwamna mai shirin barin gado, Yahya Bello ya bayyana daukar Joel a matsayin wanda zai marawa Ododo baya a matsayin aniyar tafiya da kowanne bangare na jama’ar jihar. 

Yayin jawabi lokacin gabatar da shi, malamin makarantar Joel ya ce bai san abinda zaiyi domin bayyana farincikinsa dangane da wannan karramawar da aka masa ba, na bashi damar zama mataimakin gwamna a karkashin jam’iyyar APC. 

A watan Maris da yagabata, an zabi malamin firamare Dr Mohammed Nasir Idris a matsayin gwamnan jihar Kebbi domin maye gurbin Abubakar Bagudu da ya kammala wa’adin shekaru 8 a karkashin jam’iyyar APC. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.