Isa ga babban shafi

DSS ta tabbatar da kama dakatatcen gwamnan bankin Najeriya

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS a Najeriya, ta tabbatar da cewar dakatatcen gwamnan babban bakin kasar Godwin Emefiele na hannun ta.

Jami'an hukumar tsaron farin kaya DSS a Najeriya.
Jami'an hukumar tsaron farin kaya DSS a Najeriya. AP - Sunday Alamba
Talla

Idan dai ba’a manta ba, bayan bullar labarin kama Emefiele da jami’an hukumar DSS suka yi, hukumar ta karya ta hakan, lamarin da ya haifar da cecetuce.

Toh sai dai a sanarwar da kakakin hukumar Peter Afunanya ya fitar a ranar Asabar din nan, ya tabbatar da cewar Emefiele na hannun su kuma ana gudanar da bincike akan sa.

Sanarnar ta bukaci kakafen yada labarai su yi taka tsantsan wajen yada abinda ya shafi lamarin.

Wasu majiyoyi masu tunshe daga fadar shugaban kasar sun tabbatarwa jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar cewar, dakatar da Emefiele da kuma kama shi na da nasaba da batun sauya fasalin takardun kudin kasar da ya yi a dai dai lokacin da ake shirin gudanar da babban zaben kasar.

Toh sai dai dakatatcen gwamnan na CBN ya musanta sabawa ka’ida bisa matakin da ya dauka, inda ya hakikance cewa aikin sa ya yi bisa tsarin doka.

A ranar Juma’ar da ta gaba ne, shugaban Najeriya Ahmed Bola Tinubu ya dakatar da Emifiele daga matsayin sa, tare da umartar sa da ya mika ragamar bankin hannun mataimakin sa da ke kulada sha’anin gudanarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.