Bankuna na sayar da dalar Amurka guda akan sama da N750 a Najeriya
Rahotanni daga Najeriya na cewa Babban Bankin kasar CBN ya janye farashin da ya kaiyade wa kudaden kasashen waje, in da ya bukaci bankunan kasuwanci da sauran masu hada-hadar kudi da su bari kasuwa ta yi halinta kan cinikin na kudaden kashen waje.
Wallafawa ranar:
Kunna - 01:37
Majiyoyin suka ce a wannan Laraba bankuna a sassan Najeriya na sayar da dalar Amurka guda akan Naira 750 ko sama da haka.
Wasu bayanai suka ce kwastomomin sun samu sakonnin Email daga wasu bankuna kan sabon matakin, ko da yake har ya zuwa wannan lokaci shafin Babban Bankin kasar CBN a yanar gizo farashi dala na kan N463/$, amma tun ranar 9 ga watan Yuni aka wallafa.
Dakatar da Emefiele
Matakin na baya-bayan nan da CBN ya dauka ya biyo bayan dakatarwar da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wa gwamnan babban bankin kasar CBN, Godwin Emefiele wanda manufofin sa na kudi suka kawowa masu zuba jari da tattalin arziki cikas da koma baya.
Hasashe na cewa farashin canjin zai iya kaiwa N800 zuwa N1000 kafin karshen wannan rana ta Laraba.
Kuna iya latsa alamar sauti da kuke ganin domin sauraron rahota akai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu