Mun kwato filaye na tiriliyoyin naira a Kano - Gwamnati
Gwamnatin Jihar Kano da ke Najeriya ta bayyana cewa ta kwato filaye na tiriliyoyin naira tun bayan da Abba Kabir Yusuf ya karbi mulkin jihar.
Wallafawa ranar:
Sabuwar gwamnatin ta rushe gine-ginen da ke Otel din Daula da filin idi da kasuwannin Kwari da Wambai da dai sauransu, al'amarin da ya haddasa cece-kuce a ciki da wajen jihar.
Gwamnatin ta zargin tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da mamaye filaye ba bisa ka'ida ba, zargin da ta musanta tare da bayyana shi a matsayin mara tushe.
Sakataren gwamnatin jihar Dr.Baffa Bichi ne ya sanar cewa, darajar kudin gine-ginen da suka rusa ta kai tiriliyoyin Naira a yayin wata hirarsa da kafar talabijin ta Channels.
Mun kwato filayen da darajarsu ta kai tiriliyoyin naira mallakin gwamnatin jihar Kano da tsohuwar gwamnati ta yi rabon su ga jamianta da iyalai. Filin sallar idi kadai, kudinsa ya kai tiriliyoyin naira. Kudin babu iyaka. Inji Dr. Bichi
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu