Isa ga babban shafi

Ana sayar da kwandon tumatur naira dubu 70 a kudancin Najeriya

Al'ummar Kudancin Najeriya na kokawa kan yadda farashin kayayyakin masarufi ya yi tsada a kwanakin nan, inda a yanzu ake sayar da kwandon tumatur akan farashin naira dubu 70 a yankin Niger Delta.

Wata mai sayar da kayan gwari a kasuwar unguwar Obalande dake birnin Legas.
Wata mai sayar da kayan gwari a kasuwar unguwar Obalande dake birnin Legas. AP - Sunday Alamba
Talla

Wata mata da ta je kasuwa domin cefanen kayan miya ta shaida wa RFI Hausa cewa, ta sayi tumatur kwaya daya akan naira 100, lamarin da ta ce ba za su iya ci gaba da jure masa ba domin kuwa ya zama dole su koma kada miyar kubewa zalla.

Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoton wakilinmu Murtala Adamu daga Calabar.

'Yan kasuwar da ke dakon tumatur din daga arewacin Najeriya zuwa kudancin kasar sun ce, dole ne farashin ya yi tashin goron zabbi ganin yadda aka kara musu kudin safarar kayan gwarin sakamakon tsadar man fetur gami da karancin tumatur din da ake da shi.

An dai samu wata annubar tsutsa wadda ta lalata akasarin tumtur din da aka noma a arewacin Najeriya a bana, abin da ya kara ta'azzara karanci da tsadar kayan gwarin a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.