Isa ga babban shafi

Najeriya: Sama da mutum 800 ne suka mutu a harin ta'addanci a watan Yuni

Sama da mutane 800 ne aka kashe cikin watan Yunin 2023 kadai, a hare-haren da masu dauke da makamai suka kaddama a sassan Najeriya kamar yadda wani sabon rahoto kan sha’anin tsaro ya tabbatar.

Gawawwakin wasu manoma kenan da mayakan Boko Haram suka kashe a ranar 29 ga watan Nuwamban 2020 a jihar Bornon Najeriya.
Gawawwakin wasu manoma kenan da mayakan Boko Haram suka kashe a ranar 29 ga watan Nuwamban 2020 a jihar Bornon Najeriya. AP - Jossy Ola
Talla

Wata kungiya mai suna Beacon Consulting da ke bibiyar bayanan sirri da na tsaro, rahoton ta ya nuna cewa daga cikin hare-hare 460 da aka kai, anyi garkuwa da mutum 239.

Rahoton ya ci gaba da cewa, masu dauke da makaman sun kai hare-hare a kananan hukumomi 234 da ke jihohin kassar 36 cikin kuwa har da birnin tarayyar kasar Abuja.

A jawabin da ya gabatar a wurin taron bikin rantsuwar kama aiki, shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin kawar da matsalolin da suka dabaibaye bangaren tsaro, amma cikin wata guda da karbar mulkin kasar, an samu karuwar hare-hare a sassan Najeriyar.

Har yanzu dai, gwamnatin Najeriya na neman mafita kan hare-haren masu tayar da kayar baya, masu garkuwa da mutane, da sauran matsalolin tsaro, duk da sabon nadin da aka yin a hafsoshin tsaro.

A ranar Asabar din da ta wuce kadai, kusan mutane 40 aka kashe a wasu mabanbantan hare-hare da masu dauke da makamai suka a jihohin Benue da Filato.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.