Isa ga babban shafi

An bukaci kotu ta kwace dala miliyan 129 daga hannun tsohon Gwamnan jihar Delta

Masu gabatar da kara a Birtaniya sun bukaci kotu ta bayar da umurnin kwace kudin da ya zarce Fam miliyan 100 ko kuma Dala miliyan 129 daga hannun tsohon gwamnan jihar Delta da ke Najeriya, James Ibori wanda aka samu da laifin halasta kudaden haramun a London. 

Tsohon Gwamnan jihar Delta ta Najeriya, James Ibori.
Tsohon Gwamnan jihar Delta ta Najeriya, James Ibori. © REUTERS/Estelle Shirbon/File Photo
Talla

A shekarar 2011 aka tasa keyar Ibori daga birnin Dubai zuwa London domin gurfana a gaban kotu wadda ta same shi da aikata laifuffukan da suka hada da sace dukiyar jihar sa da ke yankin Neja Delta. 

A shekarar 2012 Ibori ya amsa tuhume tuhumen da aka masa guda 10 da suka hada da zamba cikin aminci da kuma halarta kudaden haramun, abinda ya sa kotu ta yanke ma sa hukuncin daurin shekaru 13 a gidan yari. 

Bayan kwashe sama da shekaru 10 ana tafka shari’a, yanzu haka an kusa samun hukuncin alkalai na kwace wadannan makudan kudade mallakar tsohon gwamnan. 

Rahotanni sun ce alkalin kotun Crown Court da ke Southwark, David Tomlison ya bayar da umurnin karbe dukiyar, kuma tuni lauyoyin bangarorin biyu suka ga takadar, sai dai ba’a bayyana shi a bainar jama’a ba. 

Yayin zaman kotun a yau alhamis, bangarorin biyu sun gabatar da bukatar yi wa hukuncin gyara, kuma ana saran daga yau zuwa gobe juma’a mai shari’a Tomlison yayi nazari domin gabatar da hukunci akai na karshe. 

Babban mai gabatar da kara Jonathan Kinnear ya shaidawa kotun cewar kudin da ake bukatar kwacewa daga hannun Ibori sun kai Fam miliyan 101 da rabi, kuma idan yaki gabatar da su ana iya sake daure shi tsakanin shekaru 5 zuwa 10 a gidan yari. 

Shi dai Ibori ya koma Najeriya a shekarar 2017 bayan ya kwashe rabin shekarun da aka yanke masa a gidan yari, kuma bai halarci zaman kotu na yau ba. 

Kamfanin dillancin labaran Reuters yace Ibori ya shaida masa cewar zai daukaka kara akan wannan hukuncin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.