Davido ya sauke bidiyon da ke izgilanci ga ibadar Musulunci
Shahararren mawakin salon kidan Afro Beats a Najeriya, David Adeleke da aka fi sani da Davido ya cire bidiyon wata waka da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumuntar Twitter, bayan da ya fuskanci caccaka daga sassa da dama na kasar.
Wallafawa ranar:
Davido ya wallafa bidiyon wakar da wani ‘yaronsa’ da ake kira Lagos Olori ya yi ne, wanda ya yi izgilanci ga ibadar Musulunci, lamarin da bai yi wa al’ummar Musulmi dadi ba.
A ranar Asabar, Davido ya sha suka daga Musulmai da dama a dandalin sada zumuntar zamani, sakamakon wallafa wannan bidiyo mai tsawon dakikoki 45 a kafar Twitter.
Bidiyon, wanda Musulmai da dama suka bayana shi a matsayin izgilanci ga addininsu, ya nuno wani gungun mutane sanye da jallabiya, cikin suffar ibada suna Sallah, inda kwatsam suka barke da rawa da waka bayan Sallar da suke yi tun da farko.
Sun zargi mawakin da rashin nuna girmamawa ga addinin Islama, ta wajen hada ibadarsu da rawa da waka, suna mai kira a gare shi da ya nemi afuwar Musulmai.
Fitaccen jarumin wasan fina finan Hausa, Ali Nuhu na daya daga cikin dimbim Musulman da suka yi tsokaci a kan wannan batu. Zalika, ‘yan siyasa irinsu Sanata Shehu Sani da Bashir Ahmad duk sun nuna takaicinsu a kan wannan abu da Davido ya yi.
Yanzu dai an zura ido ne a gani ko Davido zai nemi afuwa a kan wannan bidiyo da ya wallafa, wanda ya janyo cece-kuce.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu