Isa ga babban shafi

Ibori zai biya Najeriya sama da Fam miliyan 100 da ya wawushe

Wata kotu a Birtaniya ta umurci wani tsohon gwamnan jihar Delta a kudu maso kudancin Najeriya, James Ibori ya biya kudin da ya kai fam miliyan 130 da ya yi sama da fadi da su a lokacin da ya  Mulki jihar.

A watan Disemba aka saki James Ibori a London
A watan Disemba aka saki James Ibori a London REUTERS
Talla

An yanke  wa James Ibori, wanda ya Mulki jihar Delta a  daga shekarar 1999 zuwa 2007 hukuncin zaman gidan yari a Birtaaniiya  a shekarar  2012 sakamakon da  laifin halasta kudaden haram da zamba cikin aminci bayan da ‘yan sandan kasar suka kama shi.

Daga nan ne masu binciken kudi daga ofishin yaki da muggan laifuka na Birtanniya suka fara daukar  matakan kwace abubuwan da ya samu da wadannan kudade da ya yi kwanciyar magirbi a kai.

A yayin zaman kotun na wannan Litinin, masu binciken sun zargi Ibori da tara kudade  masu dimbim yawa, inda alkaalin kotun ya umurce shi ya mayar wa  gwamnatin jihar Delta sama da fam miliyan 100.

Zalika, kotu ta umurci lauyan tsohon gwamnan, mazaunin Birtaniya Badresh Babulal Gohil ya mayar da kudaden da suka kai sama da fam miliyan 28.

Ibori na fuskantar hukuncin daurin shekaru 8 a gidan kaso matsawar bai yi biyayya da wannan hukuncin ba, a yayin da kotu ta bai wa Gohil watanni 6  ya biya  wadannan kudade ko ya sha zaman kaso na shekaru 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.