Isa ga babban shafi

Najeriya: Wasu mutane sun fasa rumbun ajiyar kayan abincin gwamnati a Adamawa

Gwamnan jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya, Ahmadu Finitiri ya ayyana dokar hana fita bayan da wasu mutane suka fasa rumbun ajiyar kayan abinci, mallakin Hukumar bada Agajin Gaggawa ta kasar, NEMA.

Wasu mutane sun fasa rumbun ajiyar kayan abinci na gwamnati a Adamawa.
Wasu mutane sun fasa rumbun ajiyar kayan abinci na gwamnati a Adamawa. © Daily Trust
Talla

Daga cikin kayayyakin abincin da mutanen suka diba har da wadanda gwamnatin jihar ta tanada don rage wa al’umma radadin janyen tallafin man fetur da gwamnatin kasar ta  yi.

Rahotanni sun ce akasarin wadanda suka yi wannan aika-aikar matasa ne, inda aka jiyo su suna cewa ‘mun gaji da yunwa’, a yayin da suke diba buhunan shinkafa, garaiwanin manja, kwalayen taliya da sauran kayayyaki masu mahimmanci.

‘Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa mutanen, sai dai duk da haka wasu daga cikin masu dibar ‘ganimar’  sun ci gaba da kasancewa a wajen.

Jaridar ‘Daily Trust’ da ake wallafawa a Najeriya  ta ruwaito cewa yanzu  hankali ya kwanta; saboda a halin da ake ciki, sojoji ne suka mamaye wannan wuri don tabbatar  da cewa ba a ci gaba da barna  ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.