Isa ga babban shafi

Majalisar dattijan Najeriya ta amince da ministoci 45 banda El Rufa'i

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da mutane 45 daga cikin 48 da shugaba Bola Tinubu ke neman tabbatar da su a matsayin ministocinsa.

Zauren majalisar dattijan Najeriya.
Zauren majalisar dattijan Najeriya. Twitter/@NGRSenate
Talla

Zauren majalisar ya tabbatar da mutanen 45 a matsayin mambobin majalisar ministocin sabuwar gwamnatin Tinubu ne, bayan shafe mako guda yana tantance su.

Sauran mutane uku da ake dakon ‘yan majalisar dattijan su amince da su, sun hada da tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, da Stella Okotete daga  jihar Delta, sai kuma Abubakar Danladi na jihar Taraba, wadanda ake ci gaba da gudanar da bincike kansu da ya shafi tsaro.

Mutum na karshe da ‘yan majalisar dattijan Najeriyar suka tantance shi ne Festus Keyamo, tsohon karamin ministan kwadago a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da ta gabata.

Yayin tantance Keyamo, muhawara ta yi zafi bayan da wani Sanata ya janyo hankalin majalisar akan abinda ya kira cin fuskar da Lauya Festus Keyamo ya taba yi wa majalisa, lokacin da yake rike da mukamin minista a gwamnatin da ta shude.

Dan majalisar ya ce a lokacin Keyamo da ke jagorancin shirin daukar ma’aikata a kananan hukumomin Najeriya, yayi biris da shawarar da majalisa ta gabatar da kuma kin amsa gayyatarta domin amsa tambayoyi dangane da shirin.

Daga bisani dai bayan ci gaba da zaman da suka dakatar, Keyamo ya nemi afuwar ‘yan majalisar kan laifin da suke zarginsa da aikata wa, inda  ya ce ko a wacccan lokaci sai da ya nemi afuwa akan rashin amsa gayyatar da yayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.