Isa ga babban shafi

Manoman Najeriya sun tafka asarar naira biliyan 577

Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta bayyana cewa, bangaren noma ya tafka asarar naira biliyan 577 sakamakon ambaliyar ruwan da ta mamaye jihohin kasar da dama a bara.

Manomi Ali Dan Ladi tsaye cikin gonarsa da ambaliyar ta lalata a yankin masarautar Rimgim dake jihar Jigawa mai makwaftaka da jihar Kano a arewacin Najeriya.
Manomi Ali Dan Ladi tsaye cikin gonarsa da ambaliyar ta lalata a yankin masarautar Rimgim dake jihar Jigawa mai makwaftaka da jihar Kano a arewacin Najeriya. AP - Sunday Alamba
Talla

Gwamnatin tarayya Najeriya ta ce, an bayyana adadin makuden kudaden da aka tafka asara su a cikin wani rahoto na Hukumar Kididdigar wanda kawo yanzu ba a fitar da shi ba a hukumance.

Babban Jami’in Bayar da Alkaluma na kasa, Semiu Adeniran ya ce, kafin tattara rahoton, sai da Hukumar Kididdigar ta gudanar da bincike tare da hadin guiwar Majalisar Dinkin Duniya har ma da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa, NEMA.

Binciken ya mayar da hankali ne kan jihohin Anambra da Bayelsa da Delta da Jigawa da Kogi da kuma Nasarawa.

Sai dai alkaluman sun nuna cewa, jihar Jigawa ce ta fi shan wahala, ganin yadda ambaliyar ruwan ta shafi sama da kashi 90 cikin 100 na magidanta a jihar.

Adeniran ya ce, ambaliyar ruwan ta kuma yi ta’annati ga harkokin kauswanci gami da katse wasu muhimman ayyuka, amma dai bangaren noma ne ya fi tagayya.

Matssalar dai ta haddasa karancin girbi da kashi 94, yayin da farashin kayan abinci ya yi tashin goron zabi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.