Isa ga babban shafi

Gwamnoni za su kawo cikas ga shirin raba tallafi - Kungiyar kwadago

Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun soki shirin gwamnatin kasar na baiwa jahohi naira biliyan dari da 80 don ragewa al’umma radadin cire tallafin man fetur da aka yi.

Gammayar kungiyoyin kwadago a Najeriya a yayin gangamin adawa da janye tallafin mai da gwamnatin Najeriya ta yi. Abuja, 02 ga watan Agusta, 2023.
Gammayar kungiyoyin kwadago a Najeriya a yayin gangamin adawa da janye tallafin mai da gwamnatin Najeriya ta yi. Abuja, 02 ga watan Agusta, 2023. © Daily Trust
Talla

Kungiyoyin NLC da TUC sun ce gwamnoni ba wadanda za a amince musu ba ne, domin a cewarsu naira biliyan 5 da za a baiwa kowa ce jaha ba al’umma ne za su amfana da su ba face ‘yan siyasa.

A cewar mataimakin sakataren tsare-tsare na kungiyar NLC Chris Onyeka, da kuma mataimakin shugaban kungiyar TUC Tommy Etim, idan aka yi la’akari da abinda ya faru lokacin rabon kayan tallafin annobar Conorona da aka gudanar, bai kamata a sake baiwa gwamnoni irin wannan aikin ba.

A ranar Alhamis din nan ce dai gwamnatin kasar ta sanar da shirin rabawa gwamnatocin jahohi naira biliyan biyar-biyar da kuma tirela 180 na shinkafa, domin rabawa al’umma don samun saukin rayuwa.

Cire tallafin mai da gwamnatin Tinubu ta yi a Najeriya, ya kara jefa al’ummar kasar cikin  halin kunci sabida tsadar rayuwa.

Daga cikin hanyoyin magance radadin cire tallafin da kungiyar kwadago ta ba da shawarar samarwa, akwai batun gyara matatun man fetur din kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.