Jagoran rikicin kabilanci tsakanin mayakan Boko Haram ya mika kansa ga sojoji
Kwamandan kungiyar Boko Haram da ya haddasa rikicin kabilanci tsakanin mambobin kungiyar, wanda ya yi sanadiyar mutuwar kimanin mayaka 82, ya mika kansa ga sojoji.
Wallafawa ranar:
Wata majiyar tsaro ta tabbatarwa jaridar Dairly Trust da ake wallafawa a Najeriya cewar, Amir Bukkwaram ya mikawa sojoji kansa da iyalinsa da mayakansa da dabbobin da kuma makamansu.
A cewar majiyar, kwamandan na daga cikin manyan mayakan kungiyar ta Boko Haram, da ya sanya lungu da sako na yankin Tabkin Chadi.
Majiyar ta ce an kai Amir da mutanensa, sashi na uku na rundunar Operation Hadin kai da ke garin Monguno na jahar Borno.
Idan ba a manta ba, a ranar Alhamis ne labarin rikicin kabiyanci tsakanin mayakan Boko Haram din da ya kaure a tsibitin Bukkwaram ya bayyana, inda kusan 82 suka mutu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu