Isa ga babban shafi

Matsin rayuwa ya tilasta wa magidanci rataye kansa a Jigawa

Rahotanni daga jihar Jigawa ta arewacin Najeriya sun tabbatar da yadda wani magidanci ya rataye kansa saboda tsadar rayuwa da matsanancin talaucin da yake fama da shi.

Matsalar kashe kai saboda matsin rayuwa na ci gaba da ta'azzara a tsakanin kasashen Afrika.
Matsalar kashe kai saboda matsin rayuwa na ci gaba da ta'azzara a tsakanin kasashen Afrika. AP - Massoud Hossaini
Talla

Kakakin Rundunar ‘Yan sandan Jihar DSP Lawan Shiisu Adam da ke tabbatar da hakan ga jaridar Daily Post ya bayyana sunan magidancin a matsayin Sama’ila Ilu mai shekaru 35.

A cewar rundunar ‘yan sandan jihar, da misalin karfe 11 na daren jiya Alhamis 17 ga watan Agustan da muke ciki ne ta samu rahoton yadda magidancin ya rataye kansa har lahira a kauyen Dungun Tantama da ke Karamar Hukumar Kafin Hausa ta jihar.

Kamar yadda rundunar ta bayyana, tun a ranar Laraba da ta gabata Sama’ila Ilu ya fice daga gidansa kuma ba tare da an san inda ya tafi ba, kafin daga bisani a gano gawarsa rataye a jikin bishiya.

Kakakin Rundunar ‘Yan sandan ta jihar Jigawa ya ce jami’ansu ne suka kwance gawar tare da mika ta ga asibiti don gudanar da bincike.

A cewar DSP Shiisu, tabbas bincike ya nuna magidancin ne ya rataye kansa da kansa, saboda dalilai na matsin rayuwa kuma tuni aka mika gawarsa ga ahalinsa don yi masa jana’iza bisa koyarwar addinin Islama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.