Isa ga babban shafi

Kamar Buhari, da alama Tinubu zai jagoranci ma’aikatar man fetur

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, kamar magabacinsa Muhammadu Buhari, ya bayyana a shirye yake ya jagoranci ma’aikatar albarkatun man fetur da sabuwar ma’aikatar albarkatun iskar gas ta kasa.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu via REUTERS - POOL
Talla

Shugaba Tinubu ya ba wa ministocinsa mukamai, sama da mako guda bayan da Majalisar Dattawa ta tantance su. An nada tsohon gwamnan Rivers Nyesom Wike ministan babban birnin tarayya yayin da Wale Edun ya zama ministan kudi da kuma ministan tattalin arziki. Wasu daga cikin manyan ma’aikatun sun hada da Farfesa Ali Pate, a matsayin mai kula da harkokin lafiya da walwalar jama’a, da Lateef Fagbemi a matsayin babban lauyan tarayya kuma ministan shari’a.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu © AP/Gbemiga Olamikan

An nada tsohon gwamnan Jigawa Mohammed Badaru a matsayin ministan tsaro yayin da tsohon gwamnan Kebbi Atiku Bagudu ya zama ministan kasafin kudi da tsare-tsare.

Shugaba  Bola Tinubu da magabacinsa Muhammadu Buhari
Shugaba Bola Tinubu da magabacinsa Muhammadu Buhari via REUTERS - NIGERIA'S PRESIDENCY

Sai dai shugaban bai nada ministoci da zasu jagorantar ma'aikatun albarkatun iskar gas da man fetur ba. Ko da yake bai bayyana cewa yana da niyyar rike mukamin ministan man fetur kai tsaye ba, amma rashin nada wani a wannan mukamin na nuni da cewa shugaba Tinubu na neman rike mukamin. ‘Yan Najeriya na dakon ko Shugaban kasar zai kawo sauyi ga salon tafiyarsa ko shugabanci da magabacinsa Buhari a wannan lokaci da jama’a ke fuskantar tsadar rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.