Isa ga babban shafi

Majalisar Lagos ta tsaya kan bakarta ta yin watsi da kwamishinoni

Shugaban majalisar dokokin jihar Lagos Mudashiru Obasa ya ce babu gudu babu ja da baya dangane da kin amincewa da sunayen mutane 17 daga cikin 39 da gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya tura domin tantance su a matsayin kwamishinoninsa.

Gwamnan jihar Legas, Sanwo Olu kenan, yayin karbar rantsuwar kama aiki.
Gwamnan jihar Legas, Sanwo Olu kenan, yayin karbar rantsuwar kama aiki. © sanwoOlu/Twitter
Talla

Obasa ya ce majalisar ta dauki wannan mataki ne domin kare martabar jam’iyar ta APC.

Wannan matakin da 'yan majalisar suka dauka yana neman zame musu matsala.

A zaman majalisar na ranar Litinin, Obasa ya ce babu wata barazana ko hari ko cin mutunci da zai sa su sauya matsayarsu.

Da ma dai al’ummar Musulmi a jihar ta Lagos sun gudanar da zanga-zanga kan yadda suka ce gwamnati ta mayar da su saniyar ware, musamman wajen rabon mukamai, amma hakan bai sa ta sake nazarin lamarin ba.

Musulman Lagos a harabar Majalisar Dokokin Jihar sun yi zanga-zangar kin amincewa da karancin mukaman kwamishinoni da gwamnan jihar ya bayar.
Musulman Lagos a harabar Majalisar Dokokin Jihar sun yi zanga-zangar kin amincewa da karancin mukaman kwamishinoni da gwamnan jihar ya bayar. © Daily Trust
Ko a shekarun baya an raba mukamai tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kristanci a jihar, amma alamu na nuna cewa yanzu Sanwo-Olu ya mayar da mabiya addinin Musulunci saniyar ware, inda ya zabi Musulmi 7 daga cikin mukamai 39 wanda ya tura gaban majalisar domin tantance su, kuma daga cikinsu ne a ka ki tantance 17.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.