Isa ga babban shafi

An gano yadda 'yan majalisar Najeriya ke karbar rashawa

Wani bincike ya bankado yadda jami’an Kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya da ke gudanar da bincike kan badakalar sayar da guraben ayyuka a ma’aikatu da hukumomin gwamnati ke amfani da matsayinsu wajen karbar makuden kudade a matsayin toshiyar baki daga shugabannin ma’aikatun don gudun tona musu asiri daga badakalar da suke aikatawa.

Ginin Majalisar Najeriya a Abuja.
Ginin Majalisar Najeriya a Abuja. AFP - KOLA SULAIMON
Talla

Kwamitin mai kunshe da ‘yan majalisa 39 wanda aka kafa da nufin bankado badakalar daukar aikin da ta dabaibaye ma’aikatu da hukumomin gwamnatin Najeriyar a karkashin kudirin da dan majalisa Oluwole Oke na jam’iyyar PDP ya gabatar ranar 5 ga watan Yulin da ya gabata, binciken da jaridar Premium Times ta gudanar ya nuna cewa yanzu haka kwamitin ya juye zuwa matattarar rashawa  bayan da mambobinsa ke tilasta wa shugabannin ma’aikatu biyan makuden kudade don kauce wa kwarmata sunayensu.

A baya-bayan nan ne zarge-zarge suka tsananta game da yadda kwamitin ke tatsar ma’aikatun ciki har da manyan makarantun da ke sassan kasar, bayan da bayanai ke nuna yadda makarantun ke sayar da guraben ayyuka ba tare da cancanta ko kuma tallata daukar aikin ba.

Karkashin wannan kudiri na Mr Oke da ya kai ga kafa kwamitin, akwai shirin gayyatar dukkanin shugabannin manyan makarantun Najeriya gaban kwamitin kuma wannan batu ne ya sanya su bayar da kai bori ya hau, wajen biyan makuden kudade ga kwamitin don kauce wa fallasa badakalar da suka aikata ko kuma sanya su a rahoton da kwamitin ke shirin fitarwa kan wannan bincike, kamar yadda jaridar ta ruwaito.

Sai dai jaridar ta Premium Times a Najeriyar ta ce kusan dukkanin sassan gwamnatin da wannan kwamiti ya bincika, jami’ansa sun yi amfani da damar wajen tatsar makuden kudade a matsayin na-goro ciki kuwa har da shugabannin Jami’o’in Tarayya 51 wadanda kowannensu ya biya miliyan bibbiyu a asusun ajiya mai lamba 5400495458 na Bankin Providus.

Kazalika shugabannin kwalejin kimiyya da fasaha na gwamnatin tarayya 35 da kuma shugabannin kwalejin ilimi na tarayya 27 wadanda su ma suka biya naira miliyan 3 kowannensu a matsayin toshiyar baki kan badakalar daukar aikin da suka aikata.

Premium Times ta ce a jumlace kwamitin majalisar ya karbi cin hancin da ya kai naira miliyan 267 daga iya jami’o’i da kwalejojin Ilimi kadai baya ga makuden kudaden da babu cikakkun alkalumansu daga sauran sassan da hukumomin gwamnatin Najeriyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.