Isa ga babban shafi

Atiku da Obi za su san matsayinsu kan zaben Najeriya a makon nan

Kotun da ke sauraren karar zaben shugaban kasa a Najeriya ta ayyana ranar Laraba mai zuwa a matsayin ranar da za ta yanke hukunci na karshe game da ingancin zaben watan Fabrairun da ya gabata.

A Laraba mai zuwa ne kotu a Najeriya zata yanke hukunci kan ingancin zaben shugaban kasa na watan Fabrairu.
A Laraba mai zuwa ne kotu a Najeriya zata yanke hukunci kan ingancin zaben shugaban kasa na watan Fabrairu. © Aminiya
Talla

Da yake yi wa manema labarai karin haske magatakardar kotun, Umar Bangari ne ya bayyana hakan a wannan Litinin, yana mai cewa za a baiwa ‘yan jarida damar shiga kotun sannan su yada shari’ar kai- tsaye a gidajen talabiji da rediyo.

Jam’iyyun Labour Party da kuma PDP ne suka shigar da kara kan zaben shugaban kasar, suna masu kalubalantar ingancinsa, yayin da suka bukaci kotun ta rushe sakamakon zaben da ya tabbatar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben.

Bayan hukuncin zaben shugaban kasar, ana sa ran kotunan sauraren kararrakin zaben na jihohi 25 a fadin kasar su ma su yanke hukuncin kan ingancin zaben gwamnoni da kuma ‘yan majalisar jihohi har ma da na tarayya.

Tun bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEC ta sanar da sakamakon zaben, manyan jam’iyyun adawar biyu suka yi fatali da shi, inda kuma suka ruga kotu da bukatar ko dai ta kwace nasarar Tinubu ko kuma ta umarci a sake gudanar da zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.