Isa ga babban shafi

Jam'iyyar NNPP ta kori jagoranta Rabi'u Kwankwaso

Jam'iyyar NNPP a Najeriya ta sanar da korar jagoranta Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso bayan da ta dakatar da shi makonni uku da suka gabata, sakamakon zargin sa da yi wa jam'iyyar zagon kasa tun bayan kammalla babban zaben kasar.

Rabi'u Musa Kwankwaso
Rabi'u Musa Kwankwaso © Premiumtimes
Talla

Korar Kwankwason na cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar dauke da sa hannun sSakataren Yada Labaranta na kasa  Abdulsalam Abdulrasaq.

Wannan na zuwa ne kasa da kwanaki uku bayan da wani tsagi na jam'iyyar ya sha alwashin gurfanar da tsohon gwamnan Kanon da wasu mabiyansa a gaban shari'a, sakamakon zargin wadaka da fiye da Naira biliyan 1 da aka tara a asusun jam'iyyar na kudaden sayar da fam din 'yan takara.

Sanarwar ta Abdulrasaq ta kuma kara da cewa korar Kwanwason za ta fara aiki ne nan take, yayin da ya yi karin hasken cewa, an dauki matakin ne bayan da Kwankwason ya ki bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar, sakamakon gayyatar sa da aka yi don amsa wasu tambayoyi.

Sakataren Yada Labaran jam'iyyar ya kuma tabbatar da cewa korar Rabi'u Kwankwaso na da goyon baya a cikin kundin jam'iyyar na shekarar 2022.

To sai dai da yake jam'iyyar ta rabu gida biyu kan matakin korar ta Kwankwaso, guda daga cikin masu goyon bayansa kuma mai bincken kudi na jam'iyyar Ladipo Johnson ya ce bangaren da suka kori Kwankwason ba su da alkibla kwata-kwata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.