Isa ga babban shafi

India ta zuba hannun jarin sama da dala biliyan 14 a Najeriya

India ta zuba hannun jarin dala biliyan 14 a tarayyar Najeriya.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu via REUTERS - POOL
Talla

Tuni dai shugaban Najeriyar Bola Tinubu ya yabawa matakin zuba jarin da kasar ta India ta dauka bayan wani taron hadin gwiwa da shugabannin kasashen biyu suka gudanar a birnin Delhi.

Da ya ke bayani a wajen taron, shugaban Najeriyar ya sharwaci kasashen duniya su zuba jari a Najeriya tun lokaci bai kure musu ba, yana mai tallata Najeriyar a matsayin kasa mafi bayar da romo ga abokan huldar ta.

Ta cikin wata  sanarwa da mataimakin shugaban kasar kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar, ta ce kamfanin samar da sinadaran aikin gona na Indorama shima ya amince ya sake fadada aikin sa kan kudi har Dala biliyan 8 a jihar Rivers.

Sanarwar ta kuma kara da cewa guda daga cikin manyan kamfanonin samar da karafa na India wato Jindal Steel and Power shima ya amince ya sanya hannun jarin dala biliyan 3 a Najeriya.

Kamfanin SkipperSeil shima ya yi alkawarin zuba jarin Dala biliyan 1 da miliyan 600 don samar da wutar lantarki mai karfin mega whats 100 a wasu daga cikin jihohin arewacin Najeriyar, yayin da zai kara karfin ta zuwa Mega Whats 2000 cikin shekaru 4 masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.