INEC na da damar fayyace tsarin fitar da sakamakon zabe - Kotu
Kotun da ke sauraren kararkin zaben Najeriya ta ce baya cikin dokokin hukumar zaben kasar cewa dole sai hukumar zaben mai zaman kanta INEC ta rika bayyana sakamakon zabe a fili.
Wallafawa ranar:
Yayin yanke hukuncin, mai shari’a Haruna Tsammani ya ce dokokin da suka samar da INEC sun bata damar zabar yadda take sha’awar ayyana sakamakon zabe, ko dai ta barshi ga jama’a su rika gani tun daga matakin mazaba ko kuma ta bari sai an gama tattarawa gaba daya.
Ko da ya ke karanto sashe na 52 da 65 na dokokin da suka kafa hukumar INEC sun ce babu damar wata hukuma ko kuma Kotu su yiwa INEC katsalandan game da yadda zata tattara da kuma ayyana sakamakon zabe.
Alkalin na wadannan bayanai ne a lokacin da yake jingine karar jam’iyyar Labour kan cewa INEC ta yi kumbiya-kumbiya wajen ayyana sakamakon a shafukan yanar gizo tun daga matakin mazaba.
Har yanzu dai kotun bata gai ga yanke hukuncin karshe kan kararrakin da aka shigar ba, sai dai ana sanya ran a yau din ne zata kammalla ta kuma fitar da hukunci na karshe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu