Isa ga babban shafi

Kotu ta tabbatar da nasarar Tinubu a zaben 2023

Kotun sauraren kararrakin zaben Najeriya ta tabbatar da Bola Ahmad Tinubu a matsayin halastaccen shugaban Najeriya, wanda ya lashe zaben da kuri’a fiye da miliyan 8.

Zababben shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu
Zababben shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu REUTERS - TEMILADE ADELAJA
Talla

Jagoran Alkalai biyar da suka jagoranci shari’ar mai shari’a Haruna Tsammani yayin da yake karanto hukuncin ya ce Bola Tinubu ya bi duk wasu ka’idoji na tsayawa takara, kuma ya cika ka’idojin cin zabe.

Wannan dai na zuwa ne bayan da kotun ta tsefe dukannin zarge-zargen da manyan jam’iyyun wato PDP da Labour ke yi masa, inda ta bisu daya bayan daya ta warware kana ta jingine su.

A yayin zaman Kotu na tsahon fiye da sa’o’i 12 kotun ta kuma wanke Bola Tinubu kan zarge-zargen badakalar kudi da  tu’ammali da miyagun kwayoyi da kuma almundahana a takardun karatun sa.

Wannan dai na nufin Bola Ahmad Tinubu yayi nasara a kotu, kuma zai ci gaba da zama halastaccen shugaban kasar har tsahon shekaru 4 masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.