Isa ga babban shafi
labarin aminiya

Za a yi kiɗan kwarya da na shantu yayin auren zawarawa a Kano – Daurawa

Shugaban hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce za a yi kidan ƙwarya da na shantu domin nishaɗantar da zawarawan da za yi bikinsu a Jihar.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa. © AfricaTV3
Talla

Ya bayyana hakan ne yayin da yake karin haske a kan shirye-shiryen aurar da zawarawa da ’yan mata 1,800 da gwamnatin Jihar ke kokarin yi.

A cewar Sheikh Daurawa, za a yi shagulgula iri-iri domin nishadantar da ma’auratan, tun da a cewarsa, addinin Musulunci bai hana ba.

Ya ce, “Za mu gayyato masu kidan ƙwarya da na shantu da duk wani nau’i na nishadi da Musulunci ya amince da shi.

“Amma ba za mu bar kowa ya shiga da waya ba saboda kada a ɗauki matan mutane suna nishadi,” in ji shugaban na Hisbah.

Ya kuma ce sun ware wa kowacce daga cikin Ƙananan Hukumomin Jihar 44 Naira dubu 500 domin shagulgulan nishadi a yayin biki.

Gwamnatin Jihar dai ta ware sama da miliyan 800 domin bikin zawarawan.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin ba ta sanar da ranar da za a yi bikin ba, amma ta ce tana ci gaba da shirye-shirye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.