Isa ga babban shafi

Hadarin kwale-kwale ya kashe kusan mutum dubu guda a Najeriya cikin shekaru 3

Wata kididdiga da jaridar Daily Trust ta Najeriya ta tattara ya nuna cewa mutane 936 ne suka mutu a sakamakon kifewar kwale-kwale ko kananan jiragen ruwa a Najeriya cikin shekaru 3.

Wannan matsala na ci gaba da jefa faragaba a zukatan mazauna kayuka musamman wadanda basu da zabi illa amfani da sufurin ruwa.
Wannan matsala na ci gaba da jefa faragaba a zukatan mazauna kayuka musamman wadanda basu da zabi illa amfani da sufurin ruwa. © AP/Leo Correa
Talla

Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu ya bada umarnin gudanar da bincike kan dalilin faruwar hadarin kwale-kwalen barakatai a kasar.

Kididdigar ta nuna cewa rashin kyawu ko kuma tsaftar kogunan da ake da su a kasar na cikin manyan dalilan da ke haddasa hadarin, la’akari da  yadda tarkace ya yi yawa cikin mafi yawan manyan kogunan da ake da su a kasar.

Amfani da tsaffin jiragen ruwan katako da suka ji jiki shima wata babbar matsala ce da ke haddasa kifewar kwale-kwalen yayin da lodin da ya wuce kima ya zama wata babbar matsalar da aka kasa magancewa.

Daily Trust ta gano cewa duk da albarkar manyan koguna da ke da alaka da juna cikin jihohi 28 na kasar da Allah ya albarkace ta dasu, wadanda ke da tsahon fiye da kilomita dubu 10 yayin da suke karuwa da tsahon kilomita dubu 3,800 kowacce shekara, amma har yanzu matsalar mutuwa a sakamakon hadarin kwale-kwale ya ki ci yaki cinyewa.

Duk da yadda ‘yan kasuwa da manoma da ke kauyuka suka dogara da amfani da hanyar sufurin ruwa wajen isa ga kasuwanni ko kuma gonakin su, amma gwamnati ta gaza mayar da hankali wajen ceto rayukan su ta hanyar dakatar da wannan matsala.

Hadurran kwale-kwale na baya-bayan nan da aka samu sun hadar da na ranar 4 ga watan Satumabar da muke ciki, inda wani kwale-kwale dauke da mutane daga yankin Mayo-Ine da Mayo Belwa ya kife, inda mutane biyu suka mutu, kwanaki hudu bayan wannan kuma sai aka sami wani jirgin dauke da ‘yan kasuwa 23 daga kauyen Rugange na Yolan Jihar Adamawa ya kife kuma nan take mutane 15 suka ce ga garin ku nan.

Kwanaki uku bayan faruwar wannan kuma sai aka sake samun labarin mutuwar wasu mutane 30 manoma, bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya kife da su a cikin wani kogi da ke yankin Mokwa ta jihar Neja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.