Isa ga babban shafi

Bankin Duniya na bin Najeriya basuka daban daban har guda 108 - Rahoto

Wani bincike da aka gudanar ya bayyana cewar, yanzu haka akwai bashin kudade daban daban har guda 108 da gwamnatin kasar ta karba daga Bankin Duniya.

Hedikwatar Bankin Duniya da ke birnin Washington a Amurka.
Hedikwatar Bankin Duniya da ke birnin Washington a Amurka. © Wikipedia
Talla

Rahoton ya ce adadin kudaden da Bankin Duniyar kadai ke bin Najeriyar a yanzu ya kai kimanin dala biliyan 14.

Bayanan da majiyoyi suka gano daga shafin yanar gizon Bankin Duniya sun nuna cewar rancen kudi mafi dadewa wanda har yanzu Najeriya ke ci gaba da biya shi ne wanda ta karba tun a shekarar 1989 yayin shugabancin Janar Ibrahim Babangida, yayin da kuma Najeriyar ta karbi rancen baya bayan nan a shekarar 2018, karkashin jagorancin tsohuwar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Rancen mafi dadewa da Najeriya ta karba daga Bankin Duniya shi ne na dala miliyan 100 da biliyan 900 domin bunkasa ayyukan noma a kasar, tallafin da a waccan lokaci gwamnati ta yi nufin karkatar da shi ga kananan manoma.

A karkashin tsarin Bankin Duniya na karbar rancen kudade dai, Najeriya za ta fara biyan bashin da ke kanta ne, bayan shafe shekaru 5 da karba, zalika tana da damar daukar shekaru 30 kafin kammala biyan kudaden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.