Cibiyar samar da wutar lantarkin Najeriya ta sake durkushewa
Cibiyar samar da wutar lantarkin Najeriya ta sake durkushewa, kwanaki kalilan bayan fuskantar matsalar a kasa da mako guda.
Wallafawa ranar:
Bayanai sun ce karfi ko yawan wutar lantarkin da babbar cibiyar ke samarwa ya rikito daga ma’aunin megawatts dubu 3 da 594 da tsakar dare zuwa megawatt 42.7.
Wannan matsala ta zo ne kwanaki biyar bayan da babbar tashar samar da lantarkin Najeriyar da ake kira da ‘National Grid’ a turance ta durkushe har sau biyu a cikin kimanin sa'o'i 12, lamarin da ya jefa al'ummar kasar cikin duhu.
A waccan lokacin dai mahukunta sun bayyana tashin gobara a daya daga cikin muhimman sassan babbar cibiyar samar da wutar, a matsayin dalilin da ya janyo katsewar wutar lantarkin.
A wannan karon, ma dai an danganta sake rushewar cibiyar lantarkin ne da tashin wata gobara, kamar yadda ministan wutar lantarkin Adebayo Adelabu ya bayyana a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter a baya.
Ministan ya ce kwararru na kan kokarin warware matsalar da ta auku.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu