Isa ga babban shafi

Kotu a Filato ta tabbatar da nasarar gwamna Celeb Mutfwang na PDP

Kotun da ke sauraren kararrakin zaben gwamna a jihar Filato da ke tarayyar Najeriya ta tabbatarwa da gwamnan jihar Celeb Mutfwang nasarar da ya samu a zaben bana. 

Wata kasuwa a Jos a babban birnin jihar Filato a Najeriya.
Wata kasuwa a Jos a babban birnin jihar Filato a Najeriya. © Daily Trust
Talla

Mutfwang wanda ya sami nasarar karkashin jam’iyyar APC na fuskatar tuhuma daga Dr.Nentawe Yilwatda na jam’iyyar APC da ke ganin zaben cike yake da kura-kurai da kuma rashin inganci. 

Cikin bukatun jam’iyyar APC da dan takarar ta har da kira ga kotun ta amince da wasu kuri’u na mazabu 14 da hukumar INEC ta ki amincewa da su a lokacin kirga kuri’a. 

Taswirar da ke nuna yankin Jos ta Arewa
Taswirar da ke nuna yankin Jos ta Arewa © Plateau State Government

Yayin da take yanke hukunci mai shari’a R.Irele-Ifineh ta ce dukannin shaidun da masu kara suka gabatar basu da tushe balllantana makama, don haka ta yi watsi da karrar. 

Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron rahoton da wakilinmu dake Jos Mohammed Tasiu Zakari ya aiko mana akai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.