Isa ga babban shafi

Kamfanin BUA ya rage farashin buhun siminti zuwa naira 3,500 a Najeriya

Kamfanin sarrafa siminti na BUA a Najeriya ya rage farashin buhun siminti daga naira dubu 5 zuwa naira 3,500

Shugaban kamfanin sarrafa siminiti na BUA Abdussamad Rabi'u
Shugaban kamfanin sarrafa siminiti na BUA Abdussamad Rabi'u AFP - ISSOUF SANOGO
Talla

A baya dai kamfanin na baiwa dilallai buhun simintin ne a kan naira dubu 4,650, inda ake sayar da shi a kasuwa kan naira dubu 5,000.

Ta cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar yau Lahadi, ya ce sabon farashin zai fara aiki ne daga gobe Litinin.

Kamfanin yace ya dauki matakin rage farashin ne a sakamakon sauki da ya samu wajen siyan kayayyakin da ake sarrafa siminitin da kuma kammala wasu manyan ayyukan kamfanin da ke haifar da tsadar simintin.

Kamfanin na BUA ya yi fatan wannan ragin zai zamewa ‘yan Najeriya hanyar samun sauki da kuma mallakar muhallai ba tare da wata matsala ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.