Isa ga babban shafi

Takardun karatun Tinubu ba na bogi ba ne - Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban Najeriya a karon farko, ta yi watsi da zargin da ake yi cewa takardar shedar kammala karatu da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasar INEC ta bogi ce. 

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu. 8/05/23
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu. 8/05/23 AP - Ben Curtis
Talla

Idan dai ba a manta ba, a cikin wannan makon ne Jami’ar Chicago da ke Amurka ta fitar da takardun karatun Tinubu, bayan umarnin wata kotun kasar a hukuncin da ta yanke kan karar da dan takarar jam’iyar PDP a Najeriya a zaben da ya gabata Atiku Abubakar ya shigar don samun karin hujja a zargin sahihancin takardun da ya yi. 

Duk da cewar takardar shekarar karatun Tinubu da jami’ar ta Chicago ta fitar, ba ta dauke da ranar haihuwarsa da kuma jinsi da dai sauransu, hakan ya sa ke bude wani sabon babin takaddamar da ake yi kan takardun karatun shugaban kasar.  

Toh sai dai a martanin da mai taimaka wa Tinubu wajen hulda da kafafen yada labarai Temitope Ajayi ya fitar a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter, ya ce jami’ar ta tabbatar da karatun da Tinubu ya yi a cikinta. 

Hadimin shugaban na Najeriya, ya ce tabbatar da karutu a jami’ar da ta yi, ya nuna  babu gaskiya ko kadan a zargin da ake yi cewar takardun karatun Tinubu na bogi ne. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.